SANARWA
Ana sanar da daukacin al’ummar Jihar Bauchi cewa, Insha Allahu, gobe Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, kuma ɗan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, zai iso garin Bauchi.Saboda haka, ana gayyatar magoya baya, ‘yan jam’iyya da daukacin masu fatan alheri da su taru da misalin karfe 9:00 na safe domin tarbar Mai Girma a Abubakar Tafawa Balewa International Airport.Muna roƙon kowa da ya fito cikin tsari, ladabi da bin doka domin nuna goyon baya da haɗin kai.
