Wakilan Prof. Muhammad Ali Pate, His Excellency Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, Hon. Faruk Mustafa da Bala Wunti Sun Kai Ziyarar Jaje da Tallafi ga Marasa Lafiya

Wakilan Prof. Muhammad Ali Pate, CON, His Excellency Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, Hon. Faruk Mustafa da Bala Wunti sun kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga marasa lafiyar da suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Misau zuwa Bauchi, inda ake kwantar da su a Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (Teaching Hospital), Bauchi.

Mutane hudu ne aka kwantar da su a asibitin, yayin da Allah Ya yi wa mutum bakwai rasuwa sakamakon hatsarin.

A yayin ziyarar, Prof. Muhammad Ali Pate ya ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen jinyar waɗanda ke kwance a asibiti, sannan aka ba kowane mara lafiya tallafin Naira 200,000 domin ya riƙe a hannunsa.

Wadanda suka halarci ziyarar sun haɗa da Bala Hadith, Ambassador Baba Madugu, Professor Haruna Danwanka, Muhammad Sadiq Dass, Musajo Buba, Ghali Ma’aji, Abba Sadiq (PA), Bashir Baba, tsohon Head of Service Alhaji Gokaru, da Dr. Ja’afar Dass (Technical Assistant to the Minister).

Muhammad Sadiq Dass ya wakilci Bala Wunti, Musajo Buba ya wakilci Hon. Faruk Mustafa, yayin da Prof. Haruna Danwanka, Bashir Baba, Abba Sadiq (PA) da Ghali Ma’aji suka wakilci His Excellency Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN. Bala Hadith, Ambassador Baba Madugu da Dr. Ja’afar Dass kuma sun wakilci Prof. Muhammad Ali Pate.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *