ALJERIYA TA FARA WAFCON 2026 DA NASARA KAN SENEGA

0

Ƙungiyar matan Aljeriya ta fara gasar Kofin Nahiyar Afirka ta Mata (WAFCON) ta 2026 cikin armashi bayan ta doke Senegal da ci 2-0 a wasan farko na rukuni na A da aka buga a Rabat, Morocco.

Aljeriya ta fara samun nasara ne a minti na 42, lokacin da kyaftin ɗinta, Marine Dafeur, ta zura ƙwallo ta bugun fenariti, wanda ya bai wa ƙungiyarta damar tafiya hutun rabin lokaci tana jagoranci.

Yayin da Senegal ta yi ƙoƙarin dawo wa wasan a rabin na biyu, Aljeriya ta ci gaba da nuna ƙwarewa da tsari. A minti na 88, Melissa Bethi ta ƙara ta biyu bayan da ta yi amfani da kuskuren mai tsaron ragar Senegal, Khady Faye, wajen zura ƙwallo cikin sauƙi.

Ko da yake Senegal ta fara wasan da ƙwazo tare da ƙoƙarin matsa wa abokiyar hamayyarta lamba, Aljeriya ta mamaye fafatawar a hankali kuma ta kare wasan da nasarar da ta cancanta.

__________________________________________

WAFCON 2026 na ci gaba da gudana a ƙasar Morocco, inda manyan ƙasashen nahiyar ke fafatawa domin lashe kambun zakarun Afirka a wasan ƙwallon ƙafa na mata. Wannan nasara ta bai wa Aljeriya maki uku masu muhimmanci a farkon wasanninta na rukuni, yayin da Senegal za ta nemi farfaɗowa a wasa na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *